20 Yuni 2021 - 12:00
UNHCR, Ta Damu Da Karuwar ‘Yan Gudun Hijira A Afrika Ta Tsakiya Da Yankin Sahel

Yau 20 ga watan Yuni, ita ce ranar tunawa da ‘yan gudun hijira ta duniya.

ABNA24 : Kafin wannan ranar dai Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, ta nuna matukar damuwa da karuwar ‘yan gudun hijira a duniya, musamman a Afrika ta tsakiya, da yankin sahel da kuma Uganda.

A sabon rahoton data fitar a ranar Juma’a data gabata UNHCR, ta ce yawan ‘yan gudun hijira ya karu da kashi 4 cikin dari a bara, inda ake da ‘yan gudun hijira miliyan 82, 4 adadin da ya rubanya na shekaru goma da suka gabata.

Rahoton ya ce duk da annobar korona da duniya ke fama da ita, hakan bai hana kwarara ‘yan gudun hijira ba, saboda shekarar 2020 data gabata ita ce shekara ta tara da ake fuskantar yawan ‘yan gudun hijira.

A nahiyar AFrika dai rahoton ya zayyano kasar Uganda, wacce ta fi fama da ‘yan gugun hijira, wadanda ke fama da matsalar karancin abinci wanda hakan ya tilasta rage yawan adadin abincin da ake basu.

Sai kuma wata matsalar a cewar rahoton, inda ake fuskantar ‘yan gudun hijira na cikin gida a musamman a yankin tsakiyar sahel, irinsu Burkina faso, Mali da Nijar, inda jama’a ke tserewa tashe tashen hankula masu nasaba da ‘yan ta’adda.

342/